Kwamitin bincike na rundunar sojin sama ta Najeriya kan zargin kisan fararen hula a jihohin Katsina da Zamfara ya isa jihohin domin bincike kan hakikanin abin da ya faru.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kai ziyarar, shugaban kwamitin Air Vice Marshal IG Lubo, ya ce kwamitin zai gana da dukkanin masu ruwa da tsaki a jihar.
Sannan zai gana da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu, da sarakunan gargajiya da kuma dukkanin manyan jami’an soji dake gudanar da ayyukansu a yankunan.
Ya ce rundunar sojin sama ta damu matuka a lokacin da aka bayyana zarge-zargen da ake yiwa jami’anta.
Ya kara da cewa idan har hakan ya faru ba yadda za a
yi rundunar ta boye, kuma za ta dauki matakin da ya kamata, domin magance
faruwar hakan a nan gaba, tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.