Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce ‘yan siyasa ke lalata tsarin Najeriya domin cimma wani buri na kashin kansu, bad an kishin kasa ba.
Sarkin ya bayyana hakan ne a wajen taron karawa juna sani da wata kungiyar ta shirya wanda ya gudana a Abuja.
Taron mai taken “Adalci, Dai-daito da tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, ya tattauna akan bangarori da dama da suka shafi zaman lafiya da ci gaban kasa.
Basaraken ya ce rashin gaskiya ne dalilin haddasa rikicin addinai da na kabilanci wanda a karshe kan shafi wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
Ya kara da cewa ‘yan siyasar da ke neman mulki ido rufe kan haifar da rikice-rikice a tsakanin al’umma domin su samu damar biyan bukatarsu, na darewa kan karagar mulki.
Sannan ya yi kira ga masu irin wannan hali da su ji tsoron Allah su tabbatar da cewa, ba su yi sanadiyar cutar da al’umma ba ta kowane fanni.