Home Labaru Takaddama: Majalisar Shari’a Ta Nijerita Ta Maye Gurbin Onnoghen Da Tanko Muhammad

Takaddama: Majalisar Shari’a Ta Nijerita Ta Maye Gurbin Onnoghen Da Tanko Muhammad

271
0

Majalisar kula da harkokin shari’a ta Nijeriya NJC, ta cire sunan Walter Onnoghen a matsayin shugaban alkalan Nijeriya, tare da maye gurbin sa da Tanko Muhammad a matsayin shugaban riko.

Bayanan da su ka bayyana a shafin hukumar na yanar gizo, sun nuna yadda aka cire sunan Onnoghen daga jerin sunayen mutanen da ke aiki a hukumar.

A halin yanzu dai, sunayen mutane 23 ne maimakon 24 da ke jerin ma’aikatan hukumar a karkashin jagorancin mai shari’a Muhammad Tanko.

Wannan dai ya na zuwa ne, bayan shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Onnoghen, sakamakon tuhume-tuhumen da ya ke fuskanta a kotun kula da da’ar ma’aikata bisa rashin bayyana kadarorin sa yadda ya kamata.