Home Labaru Ilimi Zargin Fasikanci: An Kori Gurbatattun Malamai 8 Daga Jami’ar Akwa-Ibom

Zargin Fasikanci: An Kori Gurbatattun Malamai 8 Daga Jami’ar Akwa-Ibom

399
0
Farfesa Ibanga
Shugaban Jami’ar Farfesa Ibanga

Jami’ar Jihar Akwa Ibom ta bayyana korar malamai 8 da aka samu da neman yin fasikanci da dalibai mata su na ba su makin jarabawa, bayan an kama su da laifin karbar kudade a hannun dalibai ta wasu manufofi da hanyoyi daban-daban.

Shugaban Jami’ar Farfesa Ibanga ya bayyana haka, a lokacin da ya ke jawabi a wani taron manema labarai da ya shirya a Ikot Akpaden da ke cikin Karamar Hukumar Enin

Ibanga, ya ce wadanda aka korar sun rika matsa wa dalibai mata da neman yin fasikanci da su a kakar karatu ta shekara ta 2015 da 2016 da kuma ta 2018 da 2019.

Ya ce daga yau sun soke yarjejeniyar daukar aiki da su ka yi wa malaman su takwas, saboda rashin kare mutuncin su da su ke yi ga dalibai mata da kuma karbar kudade a hannun dalibai.