Home Labaru Takaddama: Abin Da Ya Sa Aka Kori Ma’aikatan Osinbajo 35

Takaddama: Abin Da Ya Sa Aka Kori Ma’aikatan Osinbajo 35

252
0
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa
Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa

A farkon makonnan ne, jaridu da kafafen sada zumunta su ka dauki dumi, sakamakon labarin da ke cewa shugaba Buhari ya kori ma’aikata masu taimaka wa mataimakin sa farfesa Yemi Osinbajo 35 daga aiki.

Rahotanni sun ce  Farfesa Osinbajo na da mataimakan da su ka fi na shugaba Buhari yawa, yayin da wasu majiyoyi ke cewa an nada wasun su ne a lokacin da Osinbajo ke rikon kwarya yayin da shugaba Buhari ya kwashe samada kwanaki 130 ya na jinya a London.

Wasu Majiyoyi daga fadar shugaban kasa na cewa, korar ma’aikatan 35 ya zama dole, kasancewar an dauke wasu ayyuka ne a karkashin ofishin Osinbajo zuwa wasu ma’aikatu. Idan dai ba a manta ba, a zangon farko na mulkin shugaba Buhari, ofishin mataimakin shugaban ne ke kula da tafiyar da tattalin arzikin kasa da shirye-shiryen tallafa wa ‘yan kasa.