Home Labaru Tuna-Baya: Ban Taba Tunanin Juyin Mulki Zai Yiwu A Nijeriya Ba –...

Tuna-Baya: Ban Taba Tunanin Juyin Mulki Zai Yiwu A Nijeriya Ba – Gowon

557
0
Janar Yakubu Gowon, Tsohon Shugaban Kasa
Janar Yakubu Gowon, Tsohon Shugaban Kasa

Tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya ce bai taba tunanin cewa juyin mulki zai iya yiwuwa a Nijeriya kafin na ranar 15 Ga watan Janairu na shekara ta 1966 ba.

Bayan kisan da aka yi wa shugabanni a ranar 15 Ga watan Janairu na shekara ta 1966 Aguiyi Ironsi ya zama Shugaba na Sojoji dai, an sake yin juyin mulki biyar a Nijeriya.

Gowon ya zama shugaban kasa a ranar 29 Ga wata Yuli na shekara ta 1966 bayan kananan hafsoshin soji sun yi juyin mulki, inda Hafsoshin su ka ce sun yi juyin mulkin ne domin su yi ramuwar-gayyar kisan shugabanni da manyan sojojin Arewa.

Da ya ke tuna abin da ya faru a lokacin juyin mulkin, Gowon ya ce kafin sojoji su yi bore a ranar 15 Ga watan Janairu na shekara ta 1966, bai taba tsamammanin juyin mulki zai faru a kasar nan ba.

Janar Gowon ya bayyana haka ne, kwana daya bayan cikar sa shekaru 85 da haihuwa, a wajen bikin nada shi tare da ba shi wata lambar girmamawa.