Home Labaru Zargin Cuwa-Cuwa: Tikitin Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Kai N7,000

Zargin Cuwa-Cuwa: Tikitin Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Kai N7,000

117
0
Fasinjojin a tashar jiragen kasa ta Rigasa da ke Kaduna sun koka kan yadda suka ce ’yan bayan fage sun saye tikitin tare da tsauwala farashinsa

Fasinjojin a tashar jiragen kasa ta Rigasa da ke Kaduna sun koka kan yadda suka ce ’yan bayan fage sun saye tikitin tare da tsauwala farashinsa.

Wannan yanayi yasa fasinjoji suka rika sayen tikitin a kan farashi mai dan karen tsada daga hannun ’yan sari.

Rahotanni sunce tun a makon day a gabata ne ne shafin sayar da tikitin a intanet na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya ya daina aiki, lamarin da ya sa fasinjoji suka koma saye a tashar.

Hakan dai ya sa wasu ma’aikatan hukumar hada baki da ’yan wasu mutane inda suka saye tikitin.

Wasu bayanai sunce ana sayar da kowanne tikiti tsakanin Naira dubu uku, zuwa dubu bakwai ga fasinjoji da ke cincirindo shiga Jirgin domin kauce wa fadawa hannun masu garkuwa da mutane hanyar Kaduna zuwa Abuja ta mota.

Wani mazaunin Kaduna bayyana yadda ya sayi tikitin akan Naira 7,000 ta bayan fage.

Leave a Reply