Gwamnatin jihar Filato ta ce ta yi mamakin yadda aka kai wa Gidan yarin na Jos hari.
Kwamishinan yada labaran jihar, Dan Manjang ya ce harin na ranar Lahadi ya zo da ba-zata kasancewar gidan yarin na tsakiyar wurare masu tsaro da suka hada da ofishin ‘yansanda da na jami’an tsaron farin kaya ta DSS da kuma wata babbar kotu.
Sai dai kwamishinan bai yi bayani ba kan ko an samu rasa rai ba, inda ya ce “suna tattara bayanai kuma za mu sanar da manema labara domin kaucewa yada labaran kanzon kurege.”
A wata sanarwa da hukumar gidan gyara hali ta kasa ta fitar, ta tabbatar da faruwar al’amarin, sai dai ta ce jami’an tsaro sun yi galaba a kan maharan.
Mai Magana da yuwunta Francis Enahoro, ya ce “‘Yan bindigar kai harin ne da misalin karfe 5:20 na yammacin ranar Lahadi inda kuma suka yi musayar wuta da ma’aikatan gidan yarin.
To sai dai Enahoro ya ce sun nemi dauki daga sauran jami’an tsaro kuma nan take suka yiwa maharani kofar rago.
Daga karshe yace ya zuwa yanzu komai ya lafa inda ya bukaci jama’a dasu kwantar da hankalinsu.
You must log in to post a comment.