Home Labaru Zargin Cin Hanci: Rundunar ‘Ƴan Sandan Najeriya Ta Kama Abba Kyari

Zargin Cin Hanci: Rundunar ‘Ƴan Sandan Najeriya Ta Kama Abba Kyari

170
0

Rahotanni daga Najeriya na cewa rundunar ƴan sandan ƙasar ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda Abba Kyari.

Rahotannin sun ce a yanzu haka ana tsare da shi a sashin tattara bayanan sirri na rundunar dake Abuja.

Kawo yanzu rundunar ‘yan sandan ba ta fitar da sanarwa kan batun ba.

A watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari mai muƙamin kwamishinan ‘yan sanda bisa zargin karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid, mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala.