Home Home Zargin Safarar Hodar Ibilis: NDLEA Na Neman Dan Sanda Abba Kyari

Zargin Safarar Hodar Ibilis: NDLEA Na Neman Dan Sanda Abba Kyari

66
0

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce tana neman ɗan sanda DCP Abba Kyari ruwa a jallo kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

Wata sanarwa da NDLEA ta fitar a yau Litinin ta ce binciken ta ya nuna cewa Abba Kyari na da alaƙa da wata ƙungiya da ke safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasashen Brazil da Ethiopia zuwa Najeriya.

Sanarwar ta ce jami’an NDLEA sun gayyaci ɗan sandan don ya amsa tambayoyi game da zarge-zarge amma ya ƙi zuwa, abin da ya sa ta yi wani taron manema labaran kenan.

Ta ce Ƙin amsa kiran ta da ya yi da ƙin bata hadin kai wajen bincike shi ne dalilin da ya sa ta yi taron manema labaran a yau.

Idan ba a manta ba, a watan Yulin 2021 ne rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta dakatar da DCP Abba Kyari mai muƙamin kwamishinan ‘yan sanda bisa zargin karɓar cin hanci daga Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppid, mutumin da ke tsare a Amurka bisa zargin damfarar miliyoyin dala .