Home Labaru Zargin Almundahana: Lauyan Maina Ya Janye Daga Kare Shi A Kotu

Zargin Almundahana: Lauyan Maina Ya Janye Daga Kare Shi A Kotu

164
0

Babban kotun tarayya dake Abuja ta ba Mr. Adeola Adedipe
daman janyewa daga shari’ar almundahana da ake yi wa tsohon
shugaban kwamitin fansho, AbdulRashid Maina.

A zaman kotun da aka yi a Abuja, mai shari’a Okong Abang ya
ba lauyan daman tsame kansa saboda har yanzu wanda ya dauke
shi aiki bai biya shi kudin aikinsa ba, kuma bai san inda yake ba.

A na ci gaba da gurfanar da AbdulRashid Maina ne kan zargin
rub da ciki da kudi naira Biliyan biyu da hukumar hana
almundahana da yi wa tattalin arzikin kasa ke masa.

Hukumar yan-sandan Najeriya ta ce ta fara shirye-shiryen dawo
da tsohon shugaban kwamitin gyaran hukumar fansho,
AbdulRashid Maina, wanda aka damke a birnin Niamey
jamhuriyyar Nijar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriya, Frank
Mba, a jawabin da ya saki ya ce hukumar na kokarin ganin an
dawo dashi.

Hadakar hukumar yan sandan Najeriya da na Interpol sun
damkeshi ne bayan guduwa da ya yi daga Najeriya.

Yanzu haka ya na tsare a hannun hukumomin Nijar kafin a dawo
da shi.