Home Labaru Zabarmari: Gwamnatin Tarayya Ta Kaiwa Iyalan Manoma Kayan Abinci

Zabarmari: Gwamnatin Tarayya Ta Kaiwa Iyalan Manoma Kayan Abinci

256
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin raba
kayan tallafi ga iyalan da kisan manoma 44 da yan ta’addan
Boko Haram suka hallaka a jihar Borno.

Ministar tallafi da jin dadin jama’a, Sadiya Farouk, ta bayar da
umurnin, inda ta ce ta ziyarci jihar Borno ne tare da abokan
aikinta da takwararta, Ministar harkokin mata, Dame Pauline
Tallen, da shugaban hukumar ci gaban arewa maso gabas,
Mohammed Goni.

Ministar ta kaiwa gwamnan jihar Borno Babagana Zulum
gaisuwar ta’aziyya, sannan ta ziyarci kauyen Zabarmari a
karamar hukumar Jere domin haduwa da iyalan mamatan.

Ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin harin
kuma ya umurce kawo kayan tallafi daga gwamnatin tarayya ga
iyalan mamatan da wadanda abin ya shafa.

Kayan da aka raba musu sun hada da Buhun shinkafan dubu 13
da buhun masara dubu 13 da buhun wake dubu13 ,da galolin
man gyada 1,300 da kwalayen magi dubu 2,116 da kwalayen
tumatur na gwangwani dubu 1,083 da jakunan gishiri 650.