Home Labaru Martani: Makwaidatan Malamai Da Matsorata Aka Tara A Arewa — Naja’atu

Martani: Makwaidatan Malamai Da Matsorata Aka Tara A Arewa — Naja’atu

652
0

Wata yar gwagwarmayar mai suna Naja’atu Mohammed, ta ce
gwamnati ta gaza kare rayuka da dukiyar ‘yan Najeriya, inda ta
ce wannan gwamnati ba ta amfani kasa da komai ba.

Hajiya Naja’atu ta ce shirun manya da malaman yankin Arewa
ke sa ake ci gaba da kashe jama’a.

Ta ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ta
tausayin al’umma, musamman ‘yan Arewa, sannna kuma da
Buhari ya damu, da ya yi tankade da rairaye.

‘Yar gwagwarmayar ta ce ta sare da tafiyar gwamnatin APC
domin ba a taba satar dukiyar kasa kamar a wannan gwamnati
ba, sannan an rasa dinbin rayuka.