Home Labarai Zargin Almundahana: Kotun Abuja Ta Dage Shari’ar Jami’an Binance

Zargin Almundahana: Kotun Abuja Ta Dage Shari’ar Jami’an Binance

253
0
FILE PHOTO: Illustration shows Binance logo
FILE PHOTO: Illustration shows Binance logo

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar
halasta kuɗin haram da aka shigar kan jami’an kamfanin hada-
hadar kuɗin kirifto na Binance zuwa ranar 17 ga watan Mayu.


Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta’annati na zargin kamfanin na Binance da jami’nsa biyu, Tigran Gambarayan da Nadeem Anjarwalla da laifin halasta kuɗin haram da ya kai dala miliyan 35.4.


Lauyan Gambarayan ya shaida wa kotu cewa ba a bai wa wanda yake karewa takardun kotu ba, don haka ya roƙi kotu ta jinkirta
ƙarar. Ita ma Hukumar Tattara Haraji ta kasa FIRS tana tuhumar Binance da jami’an nasa da laifuka biyar da suka shafi kauce wa biyan haraji.

Tigran Gambarayan, wanda ɗan Amurka ne, ya musanta zargin tuhume-tuhumen da ake yi masa yayin da har yanzu ake neman abokin aikinsa, Nadeem Anjarwalla ruwa a jallo bayan ya tsere daga hannun jami’an tsaro a watan Maris.

Leave a Reply