Home Labarai Dakile Ta’Addanci: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Wanda Ya Kai Harin Jirgin Kasan...

Dakile Ta’Addanci: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Wanda Ya Kai Harin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna

111
0
CSP Prince Olumuyiwa Adejobi
CSP Prince Olumuyiwa Adejobi

Daya daga cikin ’yan bindiga da suka kai hari tare da sace
fasinjoji a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya shiga hannu
bayan shekaru biyu da faruwar lamarin
Idan dai za a iya tunawa, a shekarar 2022 ne ’yan bindiga suka
kai harin bom kan jirgin, suka yi awon gaba da mutane da dama
tare da kashe wasu.


Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce dan ta’addan mai suna Ibrahim Abdullahi, ya shiga hannun jami’anta na yaki da
masu garkuwa da mutane ne a ranar 12 ga watan Junairu, 2024 a jihar Kaduna.


Kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce, Ibrahim wanda aka fi sani da Mande, ya amsa cewa shi ne shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

ACP Adejobi ya ce, “Mande ya amsa cewa shi ne shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Leave a Reply