Home Labaru Zargi: Hukumomin Kamaru Sun Ce ‘Yan Kasuwa Da ‘Yan Siyasar Kasar Na...

Zargi: Hukumomin Kamaru Sun Ce ‘Yan Kasuwa Da ‘Yan Siyasar Kasar Na Hulda Da Boko Haram

121
0

Gwamnatin Kamaru ta ce ta gano shaidar da ke nuni da cewar mayakan kungiyar boko haram sun yi nasarar kutsa kai cikin kasar da kuma kulla hulda da wasu daga cikin ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa.

Gwamnan Jihar Arewa mai nisa Mijinyawa Bakari ya yi wannan zargi bayan da jami’an tsaro suka kamą wani tsohon dań majalisar dokokin kasar da ake zargin sa da safarar shanu ga mayakan Boko Haram da ke Najeriya.

Bakari ya ce a cikin watanni biyu da suka gabata, kungiyar na ci gaba da kulla hulda da manyan jami’an da ke yankin, kamar yadda bayanan tsaro daga bangaren hukumomi suka tabbatar.

Gwamnan ya ce wadannan mutane da ake zargi na safarar kayan abinci da kudi ga mayakan wadanda ke amfani da su wajen sayen makaman da suke kai hari da su akan fararen hula da jami’an tsaro.

Bakari bai bayyana ko mutane nawa aka kamą yanzu haka ba saboda alakar su da kungiyar, amma a makon jiya kafofin yada labaran Kamaru sun ce an kama Blama Malla, wanda tsohon dań majalisa ne saboda alaka da su, kuma yanzu haka ana tsare da shi a birnin Marwa.

Rahotanni sun ce an kama Malla ne bayan kama dan uwan sa lokacin da ya ke safarar shanu a garin Kolofata dake Yankin Mayo Sava inda mayakan suke, kuma daga bisani ya ce tsohon dan majalisar ne ya sa shi kai musu shanun guda 10.