Home Labaru Korafi: Ekong Da Omeruo Ba Su Cacanci Yi Wa Eagles Wasa Ba...

Korafi: Ekong Da Omeruo Ba Su Cacanci Yi Wa Eagles Wasa Ba – Tijjani Babangida

198
0

Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Najeriya, Tijani Babangida ya ce bai kamata ‘yan wasan da ke wasa a rukuni na 2 a Turai su samu gayyata zuwa babban tawagar kwallon kafa ta Najeriya ba.

Babangida, wanda shine shugaban kungiyar kwararrun ‘yan wasan kwallon kafa ta Najeriya, ya bayyana hakane a wata hira da manema labarai ta kafar intanet.

Kenneth Omeruo, William Troost-Ekong da Jamilu Colins na cikin ‘yan wasan da ke wasa a rukuni na biyu a Turai, kuma har yanzu ke yi wa tawagar Super Eagles ta Najeriya wasa.