Home Labaru Jimami: Mutumin Da Ya Kera Kofar Dakin Ka’aba Ya Rasu

Jimami: Mutumin Da Ya Kera Kofar Dakin Ka’aba Ya Rasu

123
0

Allah Ya yi wa mutumin da ya tsara ya kuma jagoranci kera kofar Dakin Ka’aba, Muneer Al-Jundi, rasuwa.

Hukumar Gudanarwar Masallacin Haramin Makkah ta ce Muneer da asalin kasar Syria ya rasu ne a birnin Stuttgart na kasar Jamus ranar Laraba.

Hukumar Gudanarwar Masallacin Harami sun yi addu’a Allah Ya jikan Muneer wanda a yanzu haka sunasa ke rubuce a jikink kofar Ka’aba; Allah Ya rahamshe shi.

Muneer Al Jundi, shi ne injiniyan da ya yi tsawirar sabuwar kofar Ka’abar da aka kera daga tataccen zinare shekaru 44 da suka gabata.