Home Labaru Zanga-Zangar ‘Yan Shi’a: An Tsaurara Tsaro A Abuja Da Sauran Jihohin Nijeriya

Zanga-Zangar ‘Yan Shi’a: An Tsaurara Tsaro A Abuja Da Sauran Jihohin Nijeriya

386
0
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Adamu Mohammed, Adamu ya bada umurnin tsananta tsaro a dukkan jihohin Nijeriya da babban birnin Abuja.

Hakan kuwa ya biyo bayan zanga-zangar da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da aka fi da ‘Yan Shi’a su ka rika gudanarwa a birnin Abuja.

Karanta labaru Masu Alaka: An Kashe ‘Dan Sanda Da Mai Yi Wa Kasa Hidima

Bayanin hakan, ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar ‘yan sandan Nijeriya DCP Frank Mba ya wallafa a shafun sada zumunta na na Rundunar ‘yan sandan.

Mohammed Adamu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, za a dauki matakan tsaron da su ka hada da sintiri da jiragen sama domin tabbatar da kare rayyuka da dukiyoyin ‘yan kasa baki daya.

Shugaban ‘yan sandan, ya umurci mataimakan sa da Kwamishinonin ‘Yan sanda a dukkan jihohin Nijeriya su inganta tsaro a yankunan su da jihohin su domin kare afkuwar tashin-tashina.