Home Labaru Majalisa Za Ta Binciki Gwamnatocin Obasanjo Da ‘Yar Adua Da Jonathan Da...

Majalisa Za Ta Binciki Gwamnatocin Obasanjo Da ‘Yar Adua Da Jonathan Da Buhari

322
0
Korafi: Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Fashola Domin Yin Bayanai A Kan Wasu Aikace-Aikace
Korafi: Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Fashola Domin Yin Bayanai A Kan Wasu Aikace-Aikace

Majalisar wakila ta cimma matsayar gudanar da bincike a kan makudan kudaden da gwamnatin tarayya ta biya na kwangilolin magance matsalar rashin tsayayyen hasken lantarki a Nijeriya.

Daya daga cikin ‘yan majalisar Sada Soli Jibia ya gabatar da kudurin a zauren majalisar, wanda ya samu amincewar daukacin takwarorin sa.

Karanta Labaru masu Alaka: Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Ayyukan Da Aka Ki Kammalawa

Majalisar ta ce, za a binciki tsohuwar gwamnatin Olusegun Obasanjo daga shekara ta 1999 zuwa 2007, domin bada bahasi a kan dala biliyan 16 da gwamnatin ta yi ikirarin kashewa a kan inganta wutar lantarki.

Binciken majalisar, zai kuma fadada bin kwakkwafi zuwa kan gwamnatocin marigayi Umar Musa ‘Yar Adua da Goodluck Jonathan da kuma gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Idan dai ba a manta ba, a shekara ta 2008, majalisar wakilai ta taba kaddamar da bincike a kan dala biliyan 16 da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya yi ikirarin kashewa domin inganta lantarki ba tare da ikirarin ya tabbata ba.