Home Labaru Rayuwar Makiyaya: Ina Nan Akan Baka Na Cewa Su Dawo Arewa –...

Rayuwar Makiyaya: Ina Nan Akan Baka Na Cewa Su Dawo Arewa – Farfesa Ango

456
0
Farfesa Ango Abdullahi, Babban Jigo A Kungiyar Dattawan Arewa
Farfesa Ango Abdullahi, Babban Jigo A Kungiyar Dattawan Arewa

Babban jigo a kungiyar Dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi, ya ce babu abin da zai sa ya janye daga kiran da ya yi wa makiyayan da ke zama a kudancin Nijeriya cewa su dawo arewa idan su na ganin ba su da kariya.

Farfesan dai ya jadadda matsayar sa ne a lokacin da sanata Shehu Sani ya kai masa ziyarar ban girma a gidan sa da ke Kaduna.

Sanata Shehu Sani dai ya bukaci Ango Abdullahi ya janye hukuncin kungiyar na cewa makiyaya su dawo domin ya na iya haddasa rikici, ya na mai cewa jawabin da aka alakanta dattawan arewa da shi ya haddasa rigima babba ba wai a arewa kadai ba.

Sai dai Farfesan ya ce babu abin da zai sa ya janye furcin san a cewa makiyaya su dawo Arewa, domin ya shawarce su ne idan su na ganin rayuwar su ta na cikin hatsari a kudu ba tare da kariya ba.