Home Labaru Zanga-Zanga A Faransa A Lokacin Da Ake Dakon Sanarwar Shugaban Kasar

Zanga-Zanga A Faransa A Lokacin Da Ake Dakon Sanarwar Shugaban Kasar

227
0

Dubban masu zanga-zanga kan Gwamnatin Faransa sun sake fitowa zanga zanga a karo na 22, don sake nuna bijirewar su da manufofin shugaba Emmanuel Macron, a daidai lokacin da ake jiran ya aiwatar da sauye-sauye da Gwamnatin Faransa zata gabatarwa ‘yan kasar.
A makon da ya gabata dai ne gwamnatin Faransa ta soma duba wasu daga cikin bukatun yan kasar ,bayan da aka share ‘yan kwanaki ana tafka muhara dangane da batutuwan da suka jibanci tattalin arzikin kasar .
An jima ‘yan kasar ta Faransa na kallon Gwamnatin shugaba Emmanuel Macron, a matsayin dutsen nika.
A ranar litinin da ta gabata kafafen yada labaren kasar sun share lokaci suna ta nuna ‘yan kasar a lokacin tattaunawa kai tsaye da Shugaban kasar Emmanuel Macron, inda suka nuna masa karara cewa siyasar sa ta fuskar tattalin arziki ba za ta haifar da damin ido ba.
Wasu daga cikin ‘yan kasar sun bayyana ta yada wannan gwamnati ke kokarin talautar da marasa karfi, sun kuma hango cewa masu hannu da shuni na amfana da wannan gajiya da Gwamnati take kokarin kawowa.