Home Labaru Shugaban Sashen Fikira Na Sudan Ya Yi Murabus

Shugaban Sashen Fikira Na Sudan Ya Yi Murabus

278
0

Shugaban rikon kwarya na Sudan ya sanar da ajiye mukaminsa a asabar dinnan kwana guda bayan shugaban rikon kwaryar da ya maye gurbin shugaba Omar al-Bashir ya yi murabus sakamakon ci gaban zanga-zanga a kasar ta neman mulkin farar hula ba soji ba.
Salah Abdallah Mohammed Saleh, wanda aka fi sani da Salah Gosh, shi ne mutum na biyu mai karfin fada aji a kasar bayan Omar al-Bashir, kuma shi ne ake zargi da umarnin duk kisan da jami’an tsaro suka yi lokacin zanga-zangar kasar ta fiye da watanni 4.
Tuni dai shugaban hukumar tsaro na kasar ta Sudan Laftanal Janar Abdel Fattah al-Burhan ya karbi murabus din Salah Gosh.
Yanzu haka dai al’ummar Sudan na ci gaba da bore kan lallai a samar musu da gwamnatin farar hula sabanin mulkin soji da sashen tsaron kasar ke kokarin yi.

Leave a Reply