Home Labaru India Ta Yi Makokin Cika Shekaru Da Kisan Kiyashin Amristar

India Ta Yi Makokin Cika Shekaru Da Kisan Kiyashin Amristar

390
0

Kasar India ta yi makokin cika shekaru 100 da kisan kiyashin da sojojin mulkin mallaka na Birtaniya suka yiwa al’ummar Amristar, kisan kiyashi mafi muni da tarihin India ba zai manta ba.
Kisan kiyashin da Indiyawa kewa lakabi da Jallianwala Bagh, kasar na ikirarin sojojin mulkin mallakar sun bude wuta kan fararen hula masu neman ‘yanci galibi mata da kananan yara inda suka kashe fiye da mutum dubu ko da dai Birtaniyar na cewa mutane 379 kacal aka kashe.
Cikin sakon da Firaminisatan India Narendra Modi ya gabatar ga al’ummar ta Armristar ya ce ranar babbar abin bakin ciki ne ga al’ummar kasar.
Modi wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasar, Venkaiah Naidu a wajen taron makokin cika shekaru darin ya ce makamantan cin zarafin da indiyawa suka fuskanta daga sojojin mulkin mallaka ne ke tilastasu gudanar da ayyukan da dole su kasance ababen sha’awa.
A ranar 13 ga watan Aprilun 1919 ne dai kisan kiyashin ya faru, wanda shekaru 100 kawo yanzu Birtaniya ta gaza ba da hakuri ko sanar da dalilin afkuwarsa.
Cikin jawaban jajantawa da Firaminista Theresa May ta gabatar a zaman majalisar kasar, ta nuna rashin jin dadinta da abin da ya faru shekaru 100 da suka gabata, ko da dai ta gaza aikewa da sakon neman yafiya.

Leave a Reply