Home Home Zan Gurfanar Da Waɗanda Suka Jefi Ayarin Motocina A Gaban Kotu –...

Zan Gurfanar Da Waɗanda Suka Jefi Ayarin Motocina A Gaban Kotu – Tambuwal

30
0

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa ayarin motocin sa, tare da shan alwashin gurfanar da waɗanda su ka kai harin a gaban kotu.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara ta fuskar yada labarai Muhammad Bello ya fitar, ya ce wasu da ake kyautata zaton ‘yan bangar siyasa ne su ka kai wa ayarin motocin Tambuwal hari, lokacin da ya ke komawa Sokoto daga gangamin yaƙin neman zaɓen a Ƙananan Hukumomin Wamakko da Silame.

Daga cikin waɗanda ke cikin tawagar akwai ɗan takarar gwamnan jihar Sokoto na jam’iyyar PDP Mallam Sa’idu Umar, da Janar Aminu Bande da mataimakin gwamnan jihar Sokoto Sagir Bafarawa, amma dukan su babu wanda ya ji rauni kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sai dai sanarwar ta ce, akwai motoci biyu da aka lalata a lokacin harin. Yayin zantawa da manema labarai, gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da cewa an kama wasu daga cikin waɗanda su ka kai harin kuma za a kai su kotu.