Ministan Kwadago Chris Ngige, ya karyata rahotannin da ke cewa gwamnatin tarayya ta na shirin yi wa ma’aikatan gwamnati karin albashi a shekara ta 2023.
Chris Ngige, ya ce kawai dai zancen karin alawus na ma’aikatan gwamnati amma ba albashi ba.
Ministan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, ta hannun shugaban sashen hulda da jama’a na ma’aikatar ayyuka Olajide Oshundun. Sanarwar ta kara da cewa, kwamitin fadar shugaban kasa kan albashi da ke ofishin sakataren gwamnatin tarayya, ya samu shawarwari a kan yin karin alawus ga ma’aikatan gwamnati da dama.