Home Labarai Zamfara: An Biya Kudi, An Saki ‘Yan Kasuwan Da Aka Yi Garkuwa...

Zamfara: An Biya Kudi, An Saki ‘Yan Kasuwan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Wajen Daurin Aure

80
0

Mutane 29 da aka dauke a hanyar zuwa wani daurin aure a jihar Zamfara, sun samu ‘yanci bayan kwana da kwanaki a hannun ‘yan bindiga.

Wani wanda ya ke kusa da wadanda aka dauka ya shaida wa manema labarai cewa, tuni mutanen sun bar hannun ‘yan bindiga.

Sakataren kungiyar ‘yan kasuwar waya Ashiru Zurmi, ya ce abokan aikin sa sun samu ‘yanci kuma za su koma gidajen su, sai dai bai bayyana adadin kudin da ‘yan kungiyar sa ko ‘yan’uwan mutanen su ka biya a matsayin kudin fansa ba.

Sai dai wani Abdullahi Lawal wanda dan’uwan sa ya na cikin wadanda aka dauke, ya ce sai da ‘yan’uwa su ka tara Naira dubu 330 sannan abokan aikin sa su ka tattara ragowar kudin, bayan
‘yan bindigar sun bukaci kowane dangi su tanadi Naira dubu 400.