Home Labarai Jastis Olukayode Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki Matsayin Mukaddashin CJN

Jastis Olukayode Ya Karbi Rantsuwar Kama Aiki Matsayin Mukaddashin CJN

338
0

Mai shari’a Olukayode Ariwoola na kotun koli, ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin mukaddashin shugaban alkalan Nijeriya.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya rantsar da Ariwoola yayin wani biki da aka gudanar a zauren majalisa na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Dan shekaru 62, Mai shari’a Ariwoola ya karbi aiki ne daga hannun tsohon shugaban alkalan Nijeriya Ibrahim Tanko Muhammad, kuma zai cigaba da rikon kwarya ne har zuwa lokacin da majalisar alkalai ta kasa za ta tabbatar da shi.

Yayin da ya ke daukar rantsuwar kama aiki, Ariwoola ya yi alkawarin yin aiki a kan gaskiya, da kuma biyayya ga gwamnatin tarayya tare da kare kundin tsarin mulkin Nijeriya.

Leave a Reply