Home Labarai Sababbin Bayanai Sun Fito A Kan Zargin Da Ake Yi Wa Sanata Ekweremadu...

Sababbin Bayanai Sun Fito A Kan Zargin Da Ake Yi Wa Sanata Ekweremadu Da Matar Sa

194
0

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu, ya yi karin-haske a kan zargin da hukumomin Birtaniya su ke yi ma shi na cire sassan jikin mutum ba bisa ka’ida ba.

Sanata Ike Ekweremadu ya yi ikirarin cewa ya rubuta wa ofishin jakadancin Birtaniya takarda game da dashen kodar da za a yi wa ‘yar sa.

Ekweremadu, ya sanar da kasar Birtaniya cewa tun a watan Disamba na shekara ta 2021 zai dauki nauyin bizar wanda zai bada kodar da za a dasa wa ‘yar sa Sonia Ekweremadu.

Kamar yadda ya rubuta a wasikar, Ekweremadu ya yi bayanin cewa za a yi aikin ne a asibitin Royal Free da ke birnin London.

Ya ce shi zai biya duk wasu kudi da za a bukata wajen yin dashen kodar yarinyar, sannan ya hada wa ofishin jakadancin Birtaniya takardar asusun bankin sa.

A karshen wasikar da ya aika a shekarar da ta gabata, Sanatan ya ce idan akwai wani bayani da ake bukata za a iya tuntubar shi.

Leave a Reply