Home Labaru Zamfara: Abin Da Masana Suka Ce Kan Toshe Layukan Salula

Zamfara: Abin Da Masana Suka Ce Kan Toshe Layukan Salula

225
0

Masu ruwa da tsaki su na bayyana damuwa kan matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na toshe hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara.

Tun a daren Juma’a aka toshe layukan salula a fadin jihar ta Zamfara, daga cikin matakan da hukumomi suka ɗauka na ƙoƙarin magance matsalolin tsaro a jihar.

Hukumar kula da kamfanonin sadarwa na kasa NCC ta tabbatar wa manema labarai cewa ta katse layukan salula a Zamfara bisa umarnin gwamnati.

Mutanen jihar Zamfara sun wayi gari layukansu a toshe, ba su iya kiran waya, ba a iya kiransu kuma ba su iya aika saƙo da samun damar yin musayar sakwanni ta kafofin sadarwa na intanet.

Matakin toshe layukan na salula na zuwa ne bayan ɗaukar sabbin matakan tsaro a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna da suka haɗa da hana cin kasuwar mako-mako da takaita sayar da fetur da dokar hana fitar dare a fadin Zamfara da kuma rufe makarantu.

Sai dai masana harkokin tsaro na ganin cewa an sha ɗaukar irin waɗannan matakan amma ba tare da kawo ƙarshen matsalar tsaron ba. Kuma toshe layukan sadarwar zai yi matukar tasiri ga jefa mutanen yankin cikin mawuyacin hali.

Leave a Reply