Hukumomin tsaro sun ce ‘yan bindigar da suka kashe Olajide sun sace wasu mutane biyar da suke tare da shi.
Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya lashi takubin kamo wadanda suka kashe Olajide Sowore, kani ga mawallafin jaridar Sahara Repoters, Omoleye Sowore.
A ranar Asabar wasu ‘yan bindiga suka harbe Olajide har lahira yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Benin daga Legas inda yake karatu a Jami’ar Igbinedion.
Gwamnan dai yana mai mika sakon ta’aziyyar sa ga iyalan Sowore da kuma mawallafin Sahara Reporters Omoleye Sowore bisa wannan mutuwa ta dan uwansa Olajide Sowore.
Hukumomin tsaro sun ce ‘yan bindigar da suka kashe Olajide sun sace wasu mutane biyar da suke tare da shi.
A gefe guda kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, shi ma ya yi Allah wadai da kisan Olajide.