Home Labaru Zamfara: Jiragen Saman Najeriya Sun Yi Luguden Wuta A Sansanonin ‘Yan Fashin...

Zamfara: Jiragen Saman Najeriya Sun Yi Luguden Wuta A Sansanonin ‘Yan Fashin Daji

208
0

Gwamnatin jihar Zamfara  ta yi ikirarin cewa jiragen yaƙin rundunar sojin saman kasa sun yi luguden wuta kan fitattun sansanonin ‘yan fashin daji a jihar da ma kewaye.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ta ba da sanarwar rufe abin da ta kira haramtattun tasoshin mota da wasu kasuwanni nan take a faɗin jihar.

Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Zamfara Ibrahim Dosara ya fitar ta ce sansanonin da aka tarwatsa a hare-haren sojin saman  sun haɗa da wani ƙasurgumin ɗan fashin daji da ake kira Dan ƙarami a ƙaramar hukumar shinkafi

A cewar sanarwar a baya ɗan fashin dajin ya fitar da wani bidiyo yana murna bayan artabun da suka yi da sojoji.

Mahukuntan jihar Zamfara sun kuma ce sojojin ƙasa sun yi wa wasu ‘yan fashin daji da suka yi kokarin tserewa bayan luguden wutar kwanton-ɓauna.

A baya bayan nan ne gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da umarnin toshe hanyoyin sadarwa a jihar, wanda yana cikin matakan da hukumomin suka ɗauka domin magance matsalar tsaro a jihar.

Leave a Reply