Home Labaru Zamba: INEC Ta Gargaɗi Jama’a Kan Yin Katin Zabe Ta Yanar Gizo...

Zamba: INEC Ta Gargaɗi Jama’a Kan Yin Katin Zabe Ta Yanar Gizo Na Bogi

111
0

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ja hankalin jama’a dangane da wani shafin yanar Gizo na Bogi dake yiwa mutane rajistar zaɓe na karya.

Hukumar ta yi gargaɗin ne a cikin wata sanarwa da Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Faɗakar da Masu Zaɓe na Mista Festus Okoye ya fitar a Abuja.

Okoye ya ce an ja hankalin INEC ne zuwa ga wani saƙo da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta game da wani Shafi da aka ce wai na yin rajistar masu zaɓe na INEC ne “wanda ya sha bamban da ainihin wanda hukumar INEC din ke yiwa al’umma  rajista.”

Ya ce, “Adireshin gidan yanar ƙaryar shi ne wanda ake taƙaitawa kamar haka,

Ya ce, “INEC ta na bayyana cewa ko kaɗan babu ruwan ta da wannan gidan yanar da duk wani abu da ake aikatawa a cikin sa.”

Okoye ya ce INEC ba ta ba kowace hukuma ko ƙungiya aikin ɗaukar bayanan duk wani mai niyyar yin zaɓe a madadin ta ba.

Ya ce, “Ana sanar da dukkan jama’a cewa gidan yanar da INEC ke ci gaba da gudanar da rajistar masu zaɓe a yanar gizo dai shi ne