Home Labaru Kisan Gilla: NSCIA Da MURIC Sun Yi Allah-Wadai Da Hallaka Mutum 25...

Kisan Gilla: NSCIA Da MURIC Sun Yi Allah-Wadai Da Hallaka Mutum 25 A Filato

70
0
Kisan Gilla: NSCIA Da MURIC Sun Yi Allah-Wadai Da Hallaka Mutum 25 A Filato

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya ta yi Allah-wadai da kisan matafiya Musulmai 25 da aka yi a Jos, a kan hanyarsu ta koma wa Jihar Ondo daga Bauchi ranar Asabar.

Majalisar, wacce ke karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ta sanar da haka ne a cikin wata sanarwa da babban Jami’in gudanarwar majalisar Akitek Zubairu ya fitar ranar Lahadi ya yi kira ga Musulmi da su kwantar da hankulansu kuma kada su dauki doka a hannunsu.

Anata bangaren Itama kungiyar nan mai rajin kare muradun Musulmai ta MURIC ta bukaci a gaggauta kamawa tare da hukunta duk masu hannu a kisan.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan kungiyar na kasa, Ishaq Akintola ya fitar inda ya ce, “suna Allah-wadai da kalaman Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato da takwaransa Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo wadanda suka yi ikirarin cewa wai kisan kuskure ne.