Home Labaru Mulkin Taliban: Dakarun Afghanistan Sun Mika Wuya A Filin Jirgin Kandahar

Mulkin Taliban: Dakarun Afghanistan Sun Mika Wuya A Filin Jirgin Kandahar

68
0

Kungiyar Taliban ta bayyana cewa a ƙarshe ta samu damar wargaza turjiyar da ta fuskanta a filin jirgin saman Kandahar, kuma dubban dakarun ƙasar Afghanistan, na musamman sun miƙa wuya.

Da farko dai Mayaƙan Taliban din sun fara ne da yi wa dakarun ƙawanya har tsawon kwanaki uku.

Birnin Kandahar, wanda ke kudancin ƙasar, shi ne birnin na biyu mafi girma kuma a can ne sansanin jiragen yaƙi na Bagram yake kuma can ne cibiyar rundunar sojin hadaka da Amurka ke jagoranta take.