Home Labaru Jan Kunne: Kiir Ya Gargadi Kabilun Joglein Da Pibor Su Daina Yaki...

Jan Kunne: Kiir Ya Gargadi Kabilun Joglein Da Pibor Su Daina Yaki Ko Kuma Ya Kyale Su Kashe Juna

179
0

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya ce gwamnatin sa ba zata kara jibge jami’an tsaro masu shiga tsakanin rikicin kabilanci idan yaki ya kaure a jihar Jonglein da garin Pibor na gwamnatin wurin, wani yanki da ake yawan samun mummunar arangama.

Ya ce nan gaba idan suka sake fada, ba zai kawo musu agaji ba kana ba zai kafa wani kwamiti da zai je inda aka yi yakin ba domin ya yanke shawara duk wani rikici da zai sake tashi, ba zai aike da sojoji ko ‘yan sanda ba zai kyale su su ci gaba da yaki har sai bangare daya ya gudu.

Salva Kiir ya fada a ranar Laraba, yayin da yake jawabi a wani taron zaman lafiya tsakanin kabilun Jonglei da Pibor a birnin Juba.

Masu sharhi a kan siyasa sun ce matakan da Kiir ke dauka a kan wannan batu basu dace ba, dan haka sun kira shugaban kasar da ya janye wadannan kalamai nasa.

Augustino Ting Mayai, mai nazari da sharhi a cibiyar Sudd Institute, ya ce yana sa ran shugaban ya yi wadannan kalaman ne saboda ‘yan kasa na dubi ga gwamnatin kasar ta magance irin wadannan yake yake.

Mayai ya kyautata zaton al’ummomin ba zasu dauki kalaman shugaban a matsayin dalili da zai sa su ci gaba da kaiwa juna hari.