Home Labaru Inganta Tsaro: Buhari Ya Halarci Bikin Yaye Daliban Kwalejin Horar Da Manyan...

Inganta Tsaro: Buhari Ya Halarci Bikin Yaye Daliban Kwalejin Horar Da Manyan Hafsoshin Soji

247
0
Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya samu halartar bikin yaye daliban manyan hafsoshin tsaron Nijeriya da ke birnin tarayya Abuja.

Bikin dai shi ne karo na 27 da kwalejin ta yaye daliban ta, wanda ya kunshi manyan hafsohin tsaro daga hukumomin tsaro daban-daban, musamman daga rundunar Sojin kasa, da ta ruwa da kuma ta sama.

Yayin gudanar da bikin, shugaba Buhari ya ba dalibin da ya fi hazaka daga cikin daliban da aka yaye mai suna GC OC Obadike kyauta, yayin da shi kan shi shugaban kasa ya samu kyauta daga babbar sakatariyar ma’aikatar tsaro ta Nijeriya Nuratu Batagarawa.

Nuratu Batagarawa, Permanent Sec. MOD

Daga cikin wadanda su ka halarci taron, akwai shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, da Janar Abayomi Olanisakin, da shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa Sanata Jimi Benson, da kuma Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai.

Sauran sun hada da babban hafsan sojin sama Sadique Abubakar, da babban hafsan sojin ruwa Ite Ibas, da shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu da kuma shugaban hukumar tsaro ta DSS Yusuf Magaji Bichi.