Bayan samun ‘yanci daga zaman kaso na tsawon shekaru hudu, tsohon mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Kanar Sambo Dasuki, ya ce babu wani rikici da ya shiga tsakanin shi da shugaban Buhari.
Kanar Sambo Dasuki ya shaida wa manema labarai cewa, ba ya rikici da kowa domin ya fi karfin haka, kuma ba zai iya rigima da kowa ba.
Dasuki ya gode ma wadanda su ka dage da addu’o’i har aka sake shi bayan shekaru hudu ya na tsare, sannan ya shaida wa Duniya cewa ba ya fama da wani rashin lafiya.
Ya ce ba ya da kalaman da zai iya amfani da su wajen yi wa ‘yan Nijeriya godiya, sai dai ya ce ya gode, Allah ya saka masu da alheri.
A game da batun shari’ar da gwamnati ke yi da shi a kan badakalar kudin makamai, Dasuki ya ce ya daina zuwa kotu ne saboda an bada belin shi amma gwamnati ta ki saki, amma duk lokacin da aka bada belin shi zai rika zuwa kotu domin ya kare kan shi.
Sambo Dasuki ya kara da cewa, ba ya da labarin cewa shugaba Buhari ya daure shi ne domin ramuwar gayyar abin da ya yi ma shi a lokacin juyin mulki.
You must log in to post a comment.