Home Labaru Jaje: Sanata Ahmed Lawan Ya Yi Allah Wadai Da Harin Gidan Goodluck...

Jaje: Sanata Ahmed Lawan Ya Yi Allah Wadai Da Harin Gidan Goodluck Jonathan

499
0
Goodluck Jonathan, Tsohon Shugaban Kasa

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya tir da harin da wasu Miyagu su ka kai gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya na mai bayyana lamarin a matsayin abin Allah-wadai.

Sanatan ya bayyana haka ne ta bakin mai Magana da yawun sa Ola Awoniyi a Abuja, inda ya ce kwatanta harin a matsayin dabbanci kuma karshen ta’addanci.

Shugaban majalisar ya cigaba da cewa, ya kamata duk mai hankali a Nijeriya ya yi Allah-Wadai da harin, domin ya saba wa tunani na hankali, don haka ya bukaci hukuma ta gudanar da bincike na musamman.

Sanatan, ya bukaci jami’an tsaro su gudanar da bincike domin a iya hukunta wadanda su ka yi wa Jonathan mummunan ta’adi har gidan shi, sannan ya jinjina wa kokarin Jami’an tsaron da ke bakin aiki a gidan Jonathan yayin da aka kai harin.

Leave a Reply