Sojin Nijeriya tare da ‘yan sa kai, sun yi nasarar fatattakar mayakan Boko Haram da su ka kai hari a Biu da ke Kudu da jihar Borno.
Wani jami’in farar hula na JTF ya shaida wa manema labarai yadda mayakan Boko Haram 48 su ka mutu a yakin.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Litinin da ta gabata, mayakan Boko Haram sun kai hari a garin Biu, inda su ka afka wa kauyuka uku tare da kashe mutane biyu da raunata wasu 13, amma daga bisani soji su ka fatattake su bayan musayar wuta a tsakanin su.
A washegarin jajibirin Kirsimeti da misalin karfe 6 na yamma, aka gano mayakan sun kara komawa Kimba da ke gab da garin Biu na jihar Barno, inda dakarun sojin Nijeriya su ka yi musayar wuta tsakanin su da mayakan har zuwa karfe 4 na asuba.
Bayan
nan ne, sojojin su ka duba gawarwaki, inda su ka gano sun halaka mayakan Boko
Haram 48 tare da kama wasu mutane uku daga ciki a raye.