Tsohon gwamnan jihar Abia Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana wa manema labarai yadda ake ciyar da shi a gidan gyaran hali bayan an yanke mashi hukuncin daurin shekaru 12.
Idan dai ba a manta ba, Babbar kotun tarayya da ke Legas ta yanke hukuncin ne bayan ta kama shi da laifin damfarar Naira biliyan 7 da miliyan 65 yayin da ya ke gwamnan jihar Abia.
Kamar yadda rahotanni su ka ruwaito, Kalu bai kara damuwa da halin da ya ke ciki ba, har sai lokacin da abokan sa su ka fara kai ma shi ziyara a gidan yari.
Bayan kwanaki kalilan da yanke wa Kalu hukuncin ne, wani abokin sa na kasuwanci ya kai ma shi ziyara, lamarin da ya sa ya nuna ya girgiza da halin da ya ga tsohon gwamnan a ciki.
You must log in to post a comment.