Home Labaru Jimami: MDD Ta Yi Tir Da Kisan Ma’aikatan Agaji Da Boko Haram...

Jimami: MDD Ta Yi Tir Da Kisan Ma’aikatan Agaji Da Boko Haram Ta Yi

459
0

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da kisan ma’aikatan agaji da kungiyar Boko Haram ta yi a Nijeriya.

Kisan ma’aikatan dai ya na zuwa ne, kwana biyu bayan kashe sojoji 71 na Jamhuriyar Nijar da wasu mahara su ka yi a wani kwanton-bauna, lamarin da ya tilasta wa shugaban kasar Muhamadou Issoufou katse halartar taron kasashen Afirka a kasar Masar ya koma gida.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya na ayyukan agaji da gwamantin Nijeriya sun yi tir da aika-aikar da kungiyar ta yi wa ma’aikatan agajin.Shugaba Muhammadu Buhari, ya jaddada bukatar kawo karshen miyagun ayyukan ‘yan da’addan, ya na mai cewa wajibi ne a tashi tsaye domin gani karshen danyen aikin su.

Leave a Reply