Home Labaru Wata Sabuwa: Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Kisa Bisa Laifin Kashe...

Wata Sabuwa: Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukuncin Kisa Bisa Laifin Kashe Mahaifin Sa

931
0

Wata babbar kotu da ke jihar Bauchi, ta yanke ma wani mutum mai suna Umaru Jauro-Ori hukuncin kisa, sakamakon kama shi da laifin kisan mahaifin sa cikin masallaci a kauyen Mai’aduwa da ke karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi.

Mai shari’a Aliyu Usman ya kama Jauro da laifin kisan kai ne bayan ya samu gamsassun shaidu, inda ya ce mutuwar ta biyo bayan hannun wanda ake zargi da masu gurfanarwa su ka tabbatar ta hanyar shaidu, don haka babu shakka cewa wanda ake karar ya aikata kisan kai.

Ya ce laifin ya na da hukuncin kisa ne a karkashin sashe na 221 na dokokin Penal Code, don haka ya yanke wa mai laifin hukuncin kisa.

Kamar dai yadda shaidu su ka bayyana, wanda ake zargin ya shiga masallacin ne dauke da adda ya daddatsa mahaifin sabayan an garzaya da shi babban asibitin Misau ya ce ga garin ku nan saboda miyagun raunikan da ya ji.

Alkalin ya tabbatar da cewa, Jauro ya musanta faruwar lamarin, amma masu karar sun kawo shaidu gamsassu har guda goma, kuma dan’uwan mamacin da kanin wanda ake zargin sun tabbatar wa kotu cewa shi ya kashe mahaifin sa.