Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya lashe zaben
shugaban kasar da a karon farko a tarihi aka kaiga zagaye na
biyu.
Turkiya Recep Erdogan ya shaidawa dandazon magoya bayan sa cewar, zai ci gaba da rike amanar kasar a shekaru biyar da zai ci gaba da jagoranci.
Shugaban na Turkiya ya samu mafi rinjayen kuri’u a zaben da sama da kashi 52 na kuri’un da aka kada, yayinda abokin hamayyar sa Kemal Kilicdaroglu ya samu sama da kashi 47.
Recep Tayyip Erdogan ya sha suka daga wajen ‘yan adawa, har ta kaiga sun kunlla alaka tsakanin wasu jam’iyu domin marawa Kemal Kilicdaroglu baya wanda ya zo na biyu a zaben domin kawar da jagorancin Erdogan na tsawon shekaru 20.