Jami’an tsaro a Najeriya sun cafke wasu ‘yan aware hudu da ke
fafutukar kafa kasar Yarbawa da suka kwace wani gidan rediyo
mallakin gwamnatin Najeria da ake kira Amuludun FM 99.1
Jihar Oyo.
‘Yan awaren 4 dake rajin kafa kasar yarbawa sun shiga hanun hukuma ce bisa samun su da laifin karbe ikon wata kafar yada labaru da shirye-shirye ta rediyo Najeriya Amuludun FM 99.1 a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Jami’an tsaron sun afka musu ne a yayin da suke tsaka da yada manufofin su a gidan rediyon.
Wata kafa ta shaidawa manema labarai cewa gun-gun ‘yan awaren sun kwace iko da gidan radiyon ne yayin da suka afka musu da muggan makamai da kuma kayayyakin tsafe-tsafe da misalin karfe 5 na safiyar Lahadi.
Daya daga cikin ‘yan awaren ya jikkata a yayin dauki ba dadin da aka samu tsakanin su da jami’an tsaro.














































