Akalla mutane 11 daga wata kabilar makiyaya ciki har da wani
yaro ɗan shekara huɗu suka mutu sakamakon mahaukaciyar
guguwa a arewacin Pakistan.
Dusar ƙanƙara ta faɗo a lokacin da ƴan ƙungiyar suka tsallaka wani yanki mai tsaunuka tare da garken awakin su. An kuma samu jikkatar wasu mutane 25, inda ake ci gaba da aikin ceto.
Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif ya bayyana alhinin sa game da mutuwar mutanen, inda ya ce al’amura irin su kankara na karuwa saboda sauyin yanayi.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya afku ne da sanyin safiyar ranar Asabar a wani ɓangare na hanyar da ta bi ta gundumar Astore na yankin Gilgit Baltistan zuwa makwabciyarta Azad Kashmir, a yankin Kashmir da ke karkashin Pakistan.
Babban jami’in ‘yan sanda Ziarat Ali, ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wasu mata huɗu da yaro ɗan shekara hudu na daga cikin waɗanda suka mutu. Ya ce jami’an aikin ceto sun fuskanci kalubale saboda nisa da kuma wahalar zuwa da yankin yake da shi.