Amurka ta bukaci masu ruwa da tsaki su ci gaba da aikin tabbatar da sahihin zabe da kwanciyar hankali a jihar Ondo.
Har ila yau kasar ta jadada fatan ganin an bi tsarin dimokradiya, tare da hadin-kan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da jam’iyyun siyasa da jami’an tsaro wajen daukan matakan tabbatar da cewa zaben ya gudana cikin kwanciyyar hankali da adalci a jihar.
Amurka ta ce zata cigaba da mutunta kyakyawan dangantakar dake tsakaninta da Najeriya wajen aiki tare, domin cimma muradun kasashen biyu.














































