Home Labaru Siyasa: An Bukaci Jam’iyyar PDP Da Ta Tsayar Da Dan Takara A...

Siyasa: An Bukaci Jam’iyyar PDP Da Ta Tsayar Da Dan Takara A Kudancin Kasa

199
0

Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a yankin kudu maso gabas sun yi ikirarin barin jam’iyyar matukar APC bata tsayar da ‘dan takarar shugaban kasa daga yankin su ba.

Shugabannin PDP sun lashi takobin ba za su bari dan bangaren su ya zauna a matsayin mataimakin shugaban kasa ba, kuma za su dauki duk wanda ya amsa matsayin mataimakin shugaban kasa a matsayin makiyin yankin.

Tsohon gwamna dake yankin ya sanar da manema labarai cewa tun shekarar 1998 kudu maso gabas take cikin wannan yanayin, ta na biyayya ga PDP duk da abubuwan da suka faru da tsohon mataimakin shugaban kasa, Dr Alex Ekwueme a wani taro a Jos.

A cewarsu idan jam’iyyar PDP ta ki tsayar da mai takarar shugabancin kasa a 2023 daga yankin kudu maso gabas, dole za mu bar jam’iyyar.

Muna bayan dan uwanmu, gwamnan jihar Ebonyi David Umahi. Mun dade muna bin bayan PDP, ba zai yuwu su yi mana rikon sakainar kashi ba.

Shugabannin sun tabbatar da cewar alamu na nuna cewar jam’iyyar APC na kokarin tsayar da dan takararta daga yankin kudu maso gabas, domin haka ba za su amince da haka ba.