Home Labaru Kasuwanci Takarar Kujerar WTO: Tarayyar Turai Ta Goyi Bayan Okonjo-Iweala

Takarar Kujerar WTO: Tarayyar Turai Ta Goyi Bayan Okonjo-Iweala

258
0

Kungiyar Tarayyar Turai ta goyi-bayan takarar ‘yar Najeriya Dr Ngozi Okonjo-Iweala, a kokarin da take yin a ganin ta zama shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya WTO.

Bugu da kari Jaridar Bloomberg ta rawaito cewa gwamnatocin na Turai sun kuma amince su kada kuri’ar su ga dan takara daga Koriya ta Kudu, Yoo Myung-hee, a matsayin mutum na biyu da zai rike kungiyar.

Rahotanni sun bayyana cewa kasar Hungary ce kawai ta nuna rashin goyon-baya ga matsayin na EU ta dauka.

Yanzu haka dai Mutum biyar suka rage cikin masu gwagwarmayar neman kujerar shugabancin ta duniya.