Home Labaru Zaben Nijar: Namadi Sambo Zai Jagoranci Tawagar Kungiyar ECOWAS

Zaben Nijar: Namadi Sambo Zai Jagoranci Tawagar Kungiyar ECOWAS

232
0

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, za ta tura tawagar wakilai 90 domin sa-ido a zaben shugaban kasar Nijar da za a yi ranar Lahadi mai zuwa.

‘Yan tawagar karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Mohammed Namadi Sambo, sun fito ne daga kasashe ‘yan kungiyar guda 16.

Kafin su tafi Nijar, Shugaban ECOWAS, Mr. Jean-Claude Kassi Brou, ya jagoranci wata tawagar kwararru domin tattaunawa game da zaben a Yam ai, daga ranar 3 zuwa 4 ga watan Disamba. A ranar Lahadi 27 ga wannan watan ne, za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a Nijar, bayan cikar wa’adi na biyu na Shugaba Mahamadou Issoufou.